11/07/2026
MALAMAR DA KE CIN ƊALIBANTA 😨
Part 1 – Sabuwar Malama
Bissimillah Rahmanin RAHIM
An ce duk wani asiri yana da ranar da zai tonu...
A cikin ƙauyen Ruwan-Daji akwai wata makarantar sakandare da ake kira Gwamnatin Sakandaren Ruwan-Daji. Makaranta ce da ta yi suna wajen ilimi, kuma iyaye daga ƙauyuka da dama suna kawo 'ya'yansu domin karatu.
Sai dai a farkon zangon karatu na sabon shekara, an kawo wata sabuwar malama mai suna Maryam.
Tun ranar da ta fara zuwa makarantar, kowa ya kasa ɗauke ido a kanta.
Doguwa ce, fara ce sosai, tana da kyakkyawar fuska da murmushi mai sanya nutsuwa. Duk inda ta wuce sai kamshin turare mai daɗi ya cika wurin.
Dalibai s**a fara cewa,
"Wallahi wannan malamar ta fi kowacce kyau."
Wasu malamai ma s**a yaba da ladabinta da yadda take girmama kowa.
A cikin mako guda kacal, Malama Maryam ta zama abar so a makarantar.
Amma...
Akwai wani abu guda ɗaya da ya fara ba wasu mamaki.
Ba ta taɓa cin abinci tare da sauran malamai ba.
Idan lokacin hutun rana ya yi, sai ta rufe ƙofar ajinta daga ciki.
Idan aka buga ƙofa...
Ba ta amsawa.
Bayan kusan awa ɗaya ne take fitowa, tana gyara hijabinta k**ar ba abin da ya faru.
Wata malama mai suna Hauwa'u ta taɓa cewa,
"Maryam, kullum kina rufe kanki a aji. Lafiya kuwa?"
Maryam ta yi murmushi kawai.
"Eh Alhamdulillah... ina son shiru ne kawai."
Kowa ya ɗauka hakan dabi'arta ce.
Sai dai ba kowa ne ya yarda ba.
Akwai wani ɗalibi mai suna Sadiq.
Tun ranar farko da ya ga Maryam, zuciyarsa ta kasa amincewa da ita.
Yana jin wani irin tsoro idan ta kalle shi.
Wata rana yana wucewa kusa da ajin Malama Maryam bayan an tashi makaranta.
Sai ya ji k**ar.....akwai muryoyin yara suna kuka daga cikin ajin.
Ya tsaya cak.
Ya sake sauraro.
"Ku taimake ni..."
"Wai waye a ciki?" ya faɗa a hankali.
Da ya matsa kusa da ƙofar...
Sai muryoyin s**a yi shiru nan take.
Zuciyarsa ta fara bugawa da ƙarfi.
Ya tattara ƙarfin hali ya leƙa ta ƙaramar tagar ƙofar...
Abin da ya hango ya sa jikinsa ya yi sanyi.
Sai dai kafin ya gane sosai...
Maryam ta juya a hankali...
Idanunta s**a haɗu da nasa.
Ta yi masa murmushi...
Murmushin da bai yi k**a da na mutum ba...
A ci gaba... 😨?
Matar Talaka