JALO TV

JALO TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from JALO TV, Sardauna memorial Stadium, Kano.

Da ɗumi-ɗumi: Gwamna Uba Sani ya ƙaddamar da sabbin motocin Peugeot 3008 da 5008 na 2026.Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ub...
04/09/2026

Da ɗumi-ɗumi: Gwamna Uba Sani ya ƙaddamar da sabbin motocin Peugeot 3008 da 5008 na 2026.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya halarci taron ƙaddamar da sabbin motocin Peugeot 3008 da Peugeot 5008 na shekarar 2026 a kamfanin Dangote Peugeot Automobile Nigeria Limited (DPAN).

Gwamnan ya bayyana ƙaddamar da motocin a matsayin wata babbar alama ta ci gaban masana'antar kera motoci a Najeriya, yana mai yabawa DPAN kan jajircewarta wajen ƙirƙire-ƙirƙire, ƙarfafa masana'antu na cikin gida da bunƙasa tattalin arziki.

Gwamna Uba Sani ya ce irin waɗannan jarin suna taimakawa wajen samar da ayyukan yi, canja fasaha da kuma haɓaka ci gaban masana'antu a ƙasar.

A matsayin goyon baya ga kamfanin, gwamnan ya yi alƙawarin miƙa takardun mallakar filin DPAN, tare da cewa zai tuntubi sauran gwamnoni domin su tallafa tare da sayen motocin kamfanin a faɗin Najeriya.

Gwamna Bala Mohammed Ya Halarci Daurin Auren Ɗiyar Mataimakin Dan Takarar Shugaban Ƙasa na APMGwamnan Jihar Bauchi kuma ...
04/09/2026

Gwamna Bala Mohammed Ya Halarci Daurin Auren Ɗiyar Mataimakin Dan Takarar Shugaban Ƙasa na APM

Gwamnan Jihar Bauchi kuma Jagoran Jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) na ƙasa, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya halarci daurin auren Amina Lawal Daura, 'yar Mataimakin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyar APM, Alhaji Lawal Daura, wanda aka gudanar a garin Daura, Jihar Katsina.

Kafin daurin auren, Alhaji Lawal Daura tare da shugabannin jam'iyyar APM sun kai ziyarar girmamawa fadar Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, inda s**a nemi albarkarsa. Sarkin ya yi musu kyakkyawar tarba tare da yi wa ma'auratan addu'ar zaman lafiya da albarka.

An gudanar da daurin auren a Masallacin Jumu'a na Low Cost da ke Daura, inda manyan baƙi, shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya da sauran masu fatan alheri daga sassa daban-daban na ƙasar s**a halarta.

Daga cikin fitattun waɗanda s**a halarci taron akwai ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APM kuma Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, da ɗan takarar gwamnan Bauchi na jam'iyyar APM, Alhaji Yakubu Adamu.

A nasa jawabin, Gwamna Bala Mohammed ya taya ma'auratan da iyalansu murna, tare da addu'ar Allah Ya albarkaci aurensu da zaman lafiya, soyayya da wadata.

Wata Ƙungiyar ’Yan Gudun Hijira Mazauna Kano, Ta Ce Ba Ta Bukatar Ganin Ali Modu Sheriff a Gangamin Yaƙin Neman Zaɓen AP...
04/09/2026

Wata Ƙungiyar ’Yan Gudun Hijira Mazauna Kano, Ta Ce Ba Ta Bukatar Ganin Ali Modu Sheriff a Gangamin Yaƙin Neman Zaɓen APC

‎Wata ƙungiyar ’yan gudun hijira daga Jihar Borno da ke zaune a Kano, Borno IDPs Welfare Association, ta roƙi Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar APC da ta sake duba shirin halartar tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, a gangamin yaƙin neman zaɓe da za a gudanar ranar Asabar a Kano.

‎A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 4 ga Satumba, 2026, da aka aika wa Darakta-Janar na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC, Sanata Abdulazeez Yari, ƙungiyar ta bayyana cewa tana ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC baya, amma ta ce bayyanar Sheriff a taron na iya haifar da rashin jin daɗi a tsakanin mambobinta.

‎Ƙungiyar ta ce yawancin mambobinta mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu ne daga Borno zuwa Kano, kuma har yanzu suna ɗauke da raɗaɗin abubuwan da s**a faru a lokacin da Sheriff yake gwamnan jihar.

‎“Cikin girmamawa muna roƙon Majalisar da ta sake duba shigarsa cikin wannan taron na musamman,” in ji wasiƙar da shugabanta, Ambasada Muhammad Gana Bukar, ya sanya wa hannu.

‎Ta bayyana cewa manufarta ba ita ce ta yi watsi da APC ko neman sake zaɓen Tinubu ba, sai dai tana son a gudanar da gangamin cikin yanayin haɗin kai da kwanciyar hankali ba tare da abin da zai tayar da tsofaffin raunuka ba.

‎A cewar ƙungiyar, halartar Sheriff na iya raba kan jama’a tare da karkatar da hankali daga saƙon yaƙin neman zaɓen, har ma ya sa wasu daga cikin ’yan gudun hijirar da ke goyon bayan APC su ji ba daɗi.

‎Ƙungiyar ta kuma roƙi Sanata Abdulazeez Yari da ya shiga tsakani domin tabbatar da cewa taron ya kasance mai haɗa kowa da kowa, inda ta ce tana da cikakken imani da jagorancinsa wajen ganin an gudanar da yaƙin neman zaɓen cikin nasara.

‎An aika kwafin wasiƙar ga shugaban APC na Jihar Kano ta hannun sakatariyar jam’iyyar a jihar.

‎Sanata Ali Modu Sheriff ya yi gwamnan Borno tsakanin 2003 zuwa 2011, kuma a baya ya sha musanta zarge-zargen da ke danganta shi da Boko Haram, yana mai cewa ba su da tushe.

04/09/2026

Yaran Tagwayen Mawaƙi Naira Marley Kenan Yayin Da Suke Ƙira'a

Hotunan wani Matashi Mai Tallar Tinubu A Bauchi.me za ku ce ?
04/09/2026

Hotunan wani Matashi Mai Tallar Tinubu A Bauchi.

me za ku ce ?

Rasuwar Sarkin Gumel Babban Rashi ce ga Masarautun Gargajiya da Nijeriya – Kashim ShettimaMataimakin Shugaban Ƙasa, Kash...
04/09/2026

Rasuwar Sarkin Gumel Babban Rashi ce ga Masarautun Gargajiya da Nijeriya – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Mai Martaba Alhaji Dakta Ahmed Muhammad Sani II, CON, a matsayin babban rashi ga Jihar Jigawa da Nijeriya baki ɗaya.

Shettima ya ce marigayi Sarkin ya kasance daga cikin sarakunan gargajiya da s**a sadaukar da shekaru masu yawa wajen tabbatar da zaman lafiya, bunƙasa ilimi, ci gaban al’umma da ƙarfafa haɗin kan ƴan ƙasa.

Mataimakin Shugaban Ƙasan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Jihar Jigawa, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin da Masarautar Gumel, inda ya isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin tarayya.

Marigayi Sarkin Gumel na 16 ya rasu a birnin Alkahira na ƙasar Masar a ranar 3 ga Satumba, 2026, bayan shafe kusan shekaru 46 yana mulkin masarautar. Ya hau karagar mulki ne a ranar 16 ga Disamba, 1980.

Mataimakin Shugaban Ƙasan ya ce za a tuna da marigayi Sarkin ne saboda tsawon mulkinsa, tare da hikima, zaman lafiya da kishin al’ummar da ya nuna wajen gudanar da shugabancinsa.

Ya bayyana shi a matsayin uba, mai haɗa kan jama’a, kuma mai bayar da shawarwari, wanda hikimarsa ta taimaka wajen hidimtawa al’umma da ƙasa tsawon kusan rabin ƙarni.

Shettima ya ce duk da cewa mulkin marigayin ya gudana a lokacin da Nijeriya ta fuskanci sauye-sauyen siyasa da zamantakewa da dama, ya ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, ilimi, karatun addinin Musulunci da zaman tare cikin lumana.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana matuƙar girmama marigayi Sarkin, musamman bisa gudunmawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Shettima ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi, tare da ba iyalansa, Masarautar Gumel da al’ummar Jihar Jigawa haƙurin jure wannan babban rashi.Najeriya da São Tomé za su ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu — Matawalle

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Shugaban Ƙasar São Tomé da Príncipe, Carlos Manuel Vila Nova, murnar sake zaɓensa, tare da neman ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen biyu a fannonin tsaron teku, Yankin Haɗin Gwiwa na Ci Gaban Najeriya da São Tomé, kasuwanci da zuba jari.

Tinubu, wanda Ministan Ƙasa na Tsaro, Bello Matawalle, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a birnin São Tomé, yayin bikin rantsar da Vila Nova a wa’adinsa na biyu na shekaru biyar.

Vila Nova ya samu kashi 55.88 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasar São Tomé da Príncipe da aka gudanar a ranar 19 ga Yuli.

A cikin wasiƙar taya murnar da aka miƙa wa Vila Nova, Tinubu ya ce nasarar tasa ta nuna irin amincewar da al’ummar São Tomé s**a yi da jagorancinsa.

“Mai girma Shugaba, a madadin Gwamnati da al’ummar Tarayyar Najeriya, ina taya ku murnar sake zaɓenku a matsayin Shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar São Tomé da Príncipe,” in ji Tinubu.

Shugaban ya yaba wa gwamnatin São Tomé, Hukumar Zaɓe ta ƙasar, jam’iyyun siyasa da al’ummar ƙasar bisa gudanar da zaɓen cikin lumana, sahihanci da gaskiya.

Ya ce yadda aka gudanar da zaɓen zai ƙara ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Tinubu ya ce Najeriya na matuƙar daraja kyakkyawar dangantakar da ta daɗe tana tsakanin ƙasashen biyu.

“Saboda haka, ina fatan ƙara zurfafa haɗin gwiwa a fannonin tsaron teku, Yankin Haɗin Gwiwa na Ci Gaban Najeriya da São Tomé da Príncipe, kasuwanci da zuba jari, da sauran fannoni da ke da muhimmanci ga ƙasashenmu,” in ji shi.

Matawalle ya isa filin jirgin sama na Nuno Xavier Dias International Airport da ke São Tomé a yammacin Laraba, domin wakiltar Shugaba Tinubu a bikin rantsarwar.

An gudanar da bikin ne a ginin Majalisar Dokokin ƙasar, inda shugabannin ƙasashen Afirka da Turai da sauran manyan baki s**a halarta.

Daga cikin waɗanda s**a halarci bikin akwai Shugaban Jamhuriyar Congo, Denis Sassou Nguesso; Shugaban Gabon, Brice Oligui Nguema; da Firaministar Mozambique, Maria Benvinda Levy.

Haka kuma, Ministan Harkokin Wajen Angola, Téte António, wanda ya wakilci Shugaban ƙasar; Firaministan Morocco, Aziz Akhannouch; da Firaministan Portugal, Luís Montenegro, na daga cikin mahalarta.

Tsoffin shugabannin São Tomé da Príncipe da Firaministan ƙasar, Américo Ramos, su ma sun halarci bikin rantsarwar.

Matawalle ya isar da saƙon fatan alheri daga Tinubu ga Vila Nova, tare da sake tabbatar da aniyar Najeriya na ƙara ƙarfafa dangantaka da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

04/09/2026

Kai tsaye Daga Mu'assasatu imamu malik tare da Shekh Yakub Abubakar Bauchi

Ƴan Ɗariƙa Sune Ainihin Waɗanda Suke Riƙe Da Tutar Kare Addinin Manzon Allah SAW, Saboda Duk Wani Mai Iƙrarin Izala Ko S...
04/09/2026

Ƴan Ɗariƙa Sune Ainihin Waɗanda Suke Riƙe Da Tutar Kare Addinin Manzon Allah SAW, Saboda Duk Wani Mai Iƙrarin Izala Ko Salaf, Sufaye Ne Malaman Malamansa, Domin Shekaru 50 Da S**a Wuce Babu Wata Izala A Nijeriya, Inji Ustaz Junaidu

Address

Sardauna Memorial Stadium
Kano
860211

Telephone

+2347065325698

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JALO TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to JALO TV:

Shortcuts

Share